Mark 16

Tashin Yesu daga Matattu

1Da Asabbaci ya wuce, sai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub, da kuma Salome suka sayi kayan ƙanshi domin su je su shafa wa jikin Yesu. 2A ranar farko ta mako, da sassafe, bayan fitowar rana, suna kan hanyarsu zuwa kabarin ke nan, 3sai suka tambaye juna suka ce, “Wane ne zai gungura mana dutsen daga bakin kabarin?”

4Amma da suka ɗaga kai, sai suka ga cewa, an riga an gungura dutsen. Dutsen kuwa babba ne. 5Da suna shiga cikin kabarin, sai suka ga wani saurayi sanye da farar riga, yana zaune a hannun dama, sai suka firgita.

6Ya ce, “Kada ku firgita. Kuna neman Yesu Banazare wanda aka gicciye ne. Ya tashi! Ba ya nan. Ku dubi inda aka kwantar da shi. 7Amma ku tafi ku gaya wa almajiransa da kuma Bitrus, cewa, ‘Ya sha gabanku zuwa Galili. Can za ku gan shi, kamar yadda ya faɗa muku.’ ”

8Da rawan jiki da kuma ruɗewa, matan suka fita a guje daga kabarin. Ba su kuwa gaya wa kowa ba, don suna tsoro.

9Da Yesu ya tashi daga matattu da safe, a ranar farko ta mako, ya fara bayyana ga Maryamu Magdalin, wadda ya fitar da aljanu bakwai daga cikinta. 10Ta je ta gaya wa waɗanda dā suke tare da shi, waɗanda kuma suke makoki da kuka. 11Da suka ji cewa Yesu yana da rai, har ma ta gan shi, ba su gaskata ba.

12Daga baya Yesu ya bayyana a wani kamanni dabam ga biyunsu, lokacin da suke tafiya a ƙauye. 13Waɗannan kuwa suka koma suka shaida wa sauran, amma su ma ba su gaskata ba.

14Bayan haka, Yesu ya bayyana ga Sha Ɗayan, yayinda suke cin abinci. Ya tsauta musu a kan rashin bangaskiyarsu, da yadda suka ƙi gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi.

15Ya ce, musu, “Ku tafi cikin dukan duniya, ku yi waʼazin bishara ga dukan halitta. 16Duk wanda ya gaskata, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma duk wanda bai gaskata ba kuwa, zai hallaka. 17Waɗannan alamu za su kasance tare da waɗanda suka gaskata: A cikin sunana za su fitar da aljanu, za su yi magana da sababbin harsuna. 18Za su ɗauki macizai da hannuwansu. In kuwa suka sha mugun ɗafi, ba zai cuce su ba ko kaɗan. Za su ɗibiya hannuwansu a kan marasa lafiya, su kuwa warke.”

19Bayan Ubangiji Yesu ya yi musu magana, sai aka ɗauke shi zuwa sama, ya kuma zauna a hannun dama na Allah. 20Sai almajiran suka fita, suka yi waʼazi koʼina. Ubangiji kuwa ya yi aiki tare da su, ya tabbatar da maganarsa ta wurin alamu da suke biye da maganar.

Copyright information for HauSRK